John 17

Yesu Ya Yi Adduʼa Saboda Kansa

1Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi adduʼa, ya ce:

“Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yǎ ɗaukaka ka.
2Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yǎ ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3Rai madawwami kuwa shi ne: su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. 4Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. 5Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.

Yesu Ya Yi Adduʼa Saboda Almajiransa

6“Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka. 7Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito. 8Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni. 9Ina adduʼa dominsu. Ba domin duniya nake adduʼa ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne. 10Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu. 11Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka-sunan da ka ba ni-don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yǎ cika.

13“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yǎ zama cikakke a cikinsu. 14Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba adduʼata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. 19Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.

Yesu Ya Yi Adduʼa Saboda Dukan Masu Bi

20“Adduʼata ba saboda su kaɗai ba ne. Ina adduʼa kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu, 21don dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni. 22Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya: 23Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗin kai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.

24“Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.

25“Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba ta san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. 26Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”

Copyright information for HauSRK